Skip to main content

Hausa

Mafita 275 na Cibiyar kare hakkin Dan Adam ta nahiyar Afirika wato (ACHPR) “Kariya daga cin zarafi akan abinda ya shafi jinsin mutane ko kuma ra’ayin jima’i na hakikanin gaskiya ko kuma na kashin kan mutum” an tsakuro shi ne a shekara ta 2014. Mafitar tayi Alawadai da irin cin zarafi da wasu masu ruwa da tsaki ke yi akan wadanda suka sauya jinsinsu ko kuma ra’ayin jima’i na kashin kai a wasu yankuna na nahiyar Afirika. Cibiyar ta bukaci kawo mafita tare da yin bincike tare da kawo mafita akan dukkanin nau’in cin zarafi da Jami’an tsaro ke yi akan wanda suka sauya jinsinsu ko ra’ayin jima’i.

ACHPR kungiya ce mai zaman kanta da cibiyar African Charter ta kirkiro domin kawo sauyi da kuma kare hakkin dukkanin wani mutum mazaunin nahiyar Afirika. Mafita 275 shi ne aiki na farko da kungiyar ta dauko dangane da ire-iren cin mutunci da masu ruwa da tsaki ke yi, kungiyar ta ACHPR ta tsakuro wannan take ne daga SOGI.

Mafita ta 275 akan cin-zarafi da tauye hakkin Ɗan Adam sakamakon bayyana jinsi ko ra’ayi game da jima’i.

Hukumar kare haƙƙin mutane ta Afrika (the Africa Commision) a taron da ta yi karo na 55 a Luanda dake ƙasar Angola, daga ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 12 ga watan Mayun shekara ta 2014.

Tuna baya: a muƙala ta 2 ta hukumar African Charter on Human and peoples’ Right (the African Charter) ta haramta yin wariya ga wani ko wata akan abinda ya shafi launi, ɓangaranci, jinsi, Harshe, addini, ra’ayin siyasa, asali, ko kuma matsayi.

Ci gaba da Tuna baya: a muƙala ta 3 ta hukumar African Charter ta bayyana cewa kowa yana da damar samun tsaro ƙarƙashin ikon shari’a.

Abin Lura:  muƙala ta 4 da ta 5 ta hukumar African Charter ta bayyana cewa kowa zai girmama kansa tare da girmama wanda yake tare da shi, sannan ta haramta gana-azaba da sauran muggan ayyuka da suka shafi rashin imani da kuma tsatstsauran hukunci.

Jan-Hankali: laifukan cin-zarafi, wariya da sauran laifukan da suka shafi danne hakkin Ɗan Adam na ci gaba da faruwa a nahiyar Afrika sakamakon bayyana jinsi da kuma ra’ayin jima’i da wasu ke yi.

Abin Lura: Wannan laifuka sun shafi fyaɗe, cin mutunci, gana-azaba, kisa, ɓatar da mutum da kuma ƙage.

Karin Jan-Hankali: Danne hakki da kuma cin-zarafin Ɗan Adam da wasu mahukunta ke yi a sakamakon bayyana jinsi ko ra’ayin Jima’i shi ne ya jawo Kungiyoyi masu zaman kansu fara ƙoƙarin ganin sun kawo ƙarshen matsalar.

Damuwa: Rashin hukunta wanda suke karya dokar cin-zarafi da kuma danne hakkin Dan Adam a dalilin bayyana jinsi ko ra’ayin Jima’i:

  1. Alawadai: da yadda laifukan cin-zarafi, wariya da kuma danne hakkin Ɗan Adam ke ci gaba da faruwa wanda ya haɗa da kisa, fyaɗe, cin mutunci, ɗaure mutum ba bisa ƙa’ida ba, sakamakon bayyana jinsi ko ra’ayin Jima’i.
  1. Alawadai ga Mahukunta: wannan na faruwa ne daga mahukunta wato (jami’an tsaro) akan dukkan wanda ya bayyana jinsinsa/jinsinta.
  1. Kira: ana kira ga mahukunta da kuma masu kare hakkin Ɗan Adam dasu samar da muhalli ga al’umma wanda za a zauna ba tare da tsangwama, wariya ko cin-zarafin juna ba a dalilin bayyana jinsi ko kuma abinda ya shafi ra’ayin jima’i ba.
  1. Kira ga Mahukunta: Johohi ya kamata su kawo karshen dukkanin wani nau’i na cin-zarafi da wariya da ake yiwa wanda suka bayyana jinsinsu ko da kuwa daga Jami’an tsaro ne, kuma a tabbatar da cikkaken tsaro ga kowa tare yin cikakken bincike a duk lokacin da wani lamari ya faru domin samar da nagartaccen hukunci.

Wannan an tsakuro shi ne daga wani zaman tattaunawa da hukumar kare hakkin mutane ta (the Africa commission) yayin zama na 55 da ta yi a Luanda dake ƙasar Angola a ranar 28 ga watan Afirilu zuwa 12 ga watan Mayun shekara ta 2014.

Share